Connect with us

News

Bazoum na iya fuskanta hukunci kisa ta hanyar harbin bindinga

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

Shekara ɗaya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, ƙasar na ci gaba da fuskantar sabbin ƙalubale.

Advertisement

Har yanzu dai hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum da iyalensa na tsare a hannun sojojin da suka yi juin mulki.

Ana kuma nuna damuwa kan cewa za a iya tuhumar Bazoum da laifin cin amanar ƙasa da kuma yiyuwar fuskantar hukuncin kisa.

Advertisement

Moussa Coulibaly, lauyan Bazoum, ya shaida wa sashin hausa na BBC cewa gwamnatin mulkin soji na shirin gurfanar da hambararren shugaban a wata kotu ta musamman da ba ta da ‘yancin kai da kuma nuna son kai.

Idan aka same shi da laifi, Bazoum na iya fuskantar hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga.

Advertisement

Gwamnatin ƙasar ba ta tabbatar da ko musanta wadannan zarge-zargen ba.

Shekara ɗaya bayan juyin mulkin ƙasar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani, har yanzu ba a san makomar ƙasar ba.

Advertisement

Sojojin sun hau mulki ne da alkawuran magance matsalar rashin tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar. Sai dai masana sun lura cewa duk da waɗannan alƙawuran, an kashe sojoji da dama, kuma rashin tsaro na ci gaba da yin tasiri ga rayuwar fararen hula a sassan  kasar  niger

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending