Connect with us

News

Kungiyar yorabawa ta Afenifere taja kunnan bola tinubu Kan batun dakatar da Shirin yin zanga zanga 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Kungiyar yarabawa ta Afenifere taja kunnan Shugaban  kasa bola tinubu Kan batun dakatar da Shirin yin zanga zanga sabida san zuciya da munanan manufa

 

Advertisement

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere Justice Faloye ya bayyana cewa kungiyar ta gargadi shugaba Bola Tinubu kan sakamakon aiwatar da munanan manufofinsa na tattalin arziki da ba su da inganci, wadanda suka jefa miliyoyin yan Najeriya cikin matsin rayuwa da talauci

Ba muna tada hankalin muba amma mun fahimci cewa akwai zanga-zangar da ke tafe, kuma mun fahimci cewa Hakan  ya faru ne saboda yunwar da ake fama da ita a kasar nan kuma munyi  gargadin cewa ba ma son tashin hankali. Ba mu san shugabannin da zasu hana goyon bayan zanga-zangar,” in ji kakakin Afenifere.

Advertisement

Faloye ya gargadi Mista Tinubu game da illar da ke tattare da cire tallafin man fetur, amma yana da tabbacin zai iya zuwa inda babu wata gwamnati da ta je.

Kakakin kungiyar ta Afenifere ya kara da cewa, ba wadanda ke zanga-zangar ko kuma masu son yin zanga-zanga ne ke kawo barazana ga harkokin siyasa ba. Shi ne tsarin gwamnati bola kowai

Advertisement

Ya kara da cewa, “Ba za ku iya cire tallafin irin wannan a ko’ina ba, ko da a Ingila da Amurka ko kasashe masu arziki a duniya. Idan ka cire tallafin a Ingila a yau, nan da makonni biyu, za ka ga irin wannan zanga-zangar ta fito. Don haka, a gare mu mu ce mutane su ci gaba da jin yunwa, rashin adalci ne. ”

Da aka tambaye shi ko ba ya goyon bayan Mista Tinubu kuma idan yana tunanin shugaban kasa ya gaza wa jama’a, Mista Faloye ya ce, “Tabbas, mun yi imanin cewa Shugaban zaiyi mana adalci sama-sama.

Advertisement

daga karshe dai yayi Kira da Bola tinubu daya sake fasalin tattalin arziki. Muna da tattalin arzikin tun a lokacin mulkin mallaka”.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending