Connect with us

News

Gwamnatin tarayya za ta rika siyar wa matatar man Ɗangote da ɗanyen mai kai tsaye da naira ba dala ba

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Domin tabbatar da daidaiton farashin man fetur da kuma farashin Dala da Naira, a yau Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da kudirin da Shugaba Tinubu ya gabatar na sayar da danyen mai ga Matatar Dangote da sauran matatun mai da ke tafe a Naira.

Advertisement

Matatar Dangote a halin yanzu tana bukatar tulin kago 15 na danyen mai, akan kudi dala biliyan 13.5 duk shekara. Kamfanin NNPC ya kuduri aniyar samar da guda hudu.

Dukiyar Abacha: Inda Gwamnatin Tarayya Ta Yi Kuskure

Sai dai majalisar zartaswar ta amince da cewa ganga 450,000 da za a yi amfani da su a cikin gida za a ba da su a cikin Naira ga matatun man Najeriya, ta hanyar amfani da matatar Dangote a matsayin na farko. Za a daidaita ƙimar musanya na tsawon lokacin wannan ciniki da zarar an fara bada man.

Advertisement

Wannan matsayi da gwamnati ta ɗauka zai kawar da matsalar musayar canji da kasa ke fama da shi sannan kuma naira za ta yi daraja kuma farashin mai a gidajen mai zai karye maruƙa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending