News
Zanga-zanga: Gwamnati ta fara sayar da buhun shinkafa N40,000
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta fara raba manyan motocin shinkafa goma-goma ga kowace jiha, domin sayar da kowane buhu mai nauyin kilo giram 50 a kan farashin N40,000.
Majalisar Zartarwar, FEC ta ce babu buƙatar zanga-zangar tsadar rayuwa, ta na mai cewa ana ƙoƙarin magance mafi yawancin matsalolin da masu shirya ta su ka zayyano.
Yayin da ake kusantar lokacin zanga-zangar, Shugaba Tinubu ya ce, ya na ƙoƙarin magance matsalolin matasan.
Ministan labaru, Mohammed Idris ya ce raba shinkafar wani ɓangare ne na ƙoƙarin magance matsalolin talauci da tsadar rayuwa.
Mohammed Idris, ya ce hakan ɗaya ne daga cikin abubuwa da dama da gwamnati ke yi wajen tallafa wa ƴan Nijeriya.
Ya ƙara da nuni da ƙoƙarin gwamnati na samar da tsare-tsaren bayar da aron kuɗin karatu ga ɗalibai da shirye-shiryen ɗaukar aiki, da sanya hannayen jari a harkokin noma waɗanda su na cikin buƙatun ƴan zanga-zangar.
Bugu da ƙari, ya yi kira ga ƴan zanga-zangar da su sake nazari, ya na mai cewa hakan kan iya juyawa zuwa tashin-tashina a cikin al’umma inda ya ce su ƙara haƙuri yayin da gwamnati ke ƙoƙarin shawo kan matsalolin ƙasa baki ɗaya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
