Connect with us

News

Rikicin Masarautar Kano: Sarkin Kano Na 15 Zai Yi Wa Fadar Nassarawa Kwaskwarima. 

Published

on

1725203977126
Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka na gyare-gyare a fadar Nasarawa, a yayin da ake kan ganiyar rikicin masarautara a jihar  Kano.

Sarki Aminu Ado Bayero dai yana zaune ne a karamar fadar Nasarawa tun bayan tsige shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a farkon wannan shekarar, wanda ya mayar da Sarki Sanusi II kan karagar mulki.

Shugabar Kungiyar Matan Jami’an Kwastom Ta Bude Ofishin COWA Reshen PTML

Tunanin kwaskwarimar ga fadar ya haifar da cece-ku-ce inda hakan ke nuni da aniyar sarki Bayero na ci gaba da da’awar Sarauta duk da cewa, gwamnatin jihar tuni ta tsige shi.

Dan mori na Kano, Abubakar Hassan, wanda kuma mai biyayya ne ga Sarki Aminu Bayero, ya tabbatar wa manema labarai fara kwaskwarimar ga karamar fadar. “Sarki ya fara fadada Hubbare, wacce aka fi sani da makabartar tsoffin Sarakunan Kano, kamar marigayi Sarki Abbas, ina iya tabbatar da cewa, tuni an fara aiki daga cikin gidan sarautar,” in ji Hassan.

 

Advertisement

 

Leadership

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending