Connect with us

News

Jami’ar Bayero Ta Dakatar Da Duk Wani Jadawalin Karatu Saboda Zanga-Zanga

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Bayan dogon nazari kan halin da ake ciki a Jihar Kano sakamakon Zanga-Zanga, hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta bayar da umarnin dakatar da duk wani jadawalin karatu da aka tsara nan take. Da zarar komai ya daidaita, za a ci gaba da duk wasu ayyukan ilimi da na gudanarwa cikin tsari kamar yadda aka shirya.

Advertisement

Cikin wata sanarwar da Lamara Garba, mataimakin maga takarda da harkokin Jama’a, an ba da shawarar ga ɗalibai da mazauna cikin harabar jami’ar da su kasance cikin nutsuwa da bin doka, an yi tanadi mai kyau domin tabbatar da tsaron su.

Rasha Ta Nesanta Kanta Da Masu Ɗaga Tutocin Ƙasarta A Zanga-zangar Nijeriya

Hukumar tana mai yin cikakken shiri musamman don bayar da tsaron rayuka da dukiyoyi, don haka tana jawo hankalin mambobin al’ummar jami’ar da su yi taka-tsan-tsan da yawan fita waje don kauce wa duk wani haɗari mai yiwuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending