Connect with us

News

Za A Rufe Gidajen Burodi Saboda Tsadar Fulawa Bayan Zanga-Zanga A Kano 

Published

on

DAGA NUASIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Kungiyar masu gidajen burodi ta kasa reshen jihar  Kano ta koka kan yadda ta samu karin Naira dubu 20 a duk buhu daya na fulawa a kasuwar Singa.

Advertisement

Shugaban kungiyar a Kano, Jibrin Abubakar Hamza, ya ce kafin fara zanga-zanga, suna sayen buhun fulawa daya a kan Naira dubu 65. Amma daga shekaran jiya zuwa yau, Alhamis, da aka bude kasuwar Singa, farashinta ya yi tashin gwauran zabi inda ya kai dubu 85 a duk buhu daya.

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin siyar da shinkafar tallafi ga ma’aikatan Gwamnati

Abubakar ya ce sun tuntubi kamfanin fulawa inda aka tabbatar masu da cewa buhun fulawa yana nan kan Naira dubu 60 da 450.

Advertisement

Jibrin Abubakar, ya ce tsadar ta sa su yanke shawarar rufe gidajen burodi a fadin Kano da zarar fulawa mai sauki da suke da ita ta kare.

Kungiyar masu gidajen burodi ta bukaci mahukunta su shiga cikin lamarin domin al’umma su samu saukin rayuwa.

Advertisement

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa ko a ranar Laraba, shugaban kasuwar Singa, Musa Ibrahim Na Banki, ya ce ba za su lamunci yan kasuwa marasa tsoron Allah su zuba ido suna cin karensu babu babbaka ba game da tashin farashin kayayyaki a kasuwa, inda ya ci alwashin cewa za su taka masu burki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending