News
Akalla Mutane Biyar Ne Suka Mutu Sakamakon Kifewar Wani Kwale-kwale A Jigawa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Mutum biyar sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a yankin ƙaramar hukumar Taura ta jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Alhamis, lokacin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji 20 ya kife yayin da yake ƙoƙarin tsallake kogin Gamoda a kusa da ƙauyen Nahuce.
Ɗan Wasan Ƙasar Portugal Pepe Ya Sanar Da Ritaya Daga Ƙwallon Ƙafa
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar DSP Lawan Shiisu ya tabbatar wa da BBC Faruwar lamarin, inda ya ce jami’an ‘yansadan da masu nutso da ƙwararrun ninƙaya na kan ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin da ba a gani ba.
”Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kuma kawo yanzu an ciro gawarwakin mutum biyar daga ciki, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman sauran fasinjojin kwale-kwalen 15”, in ji DSP Shiisu.
Lamarin dai na zuwa ne watanni bayan wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya janyo asarar rayuka a yankin ƙaramar hukumar Tauran.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
