News
Gwamnatin Tarayya Ta Bankaɗo Mutum 21,600 Da Ke Amfani Da Shaidar Kammala Digiri Na Boge A Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa akwai akalla mutum 21,600 da aka ɓankaɗo dake ɗauke da shaidar kammala digirin boge a faɗin Najeriya.
Mafi yawan ɗaliban dai sun samo waɗannan Satifiket ne daga Jami’o’in kasashen Togo, Benin da wasu jami’o’i dake kasashen waje.
Hukumar Haraji Ta Nemi A Samar Da Dokar Sa Ido A Kan ‘Yan Kirifto
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Ministan Ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai kan nasarorin da ya samu a ma’aikatar cikin shekara guda, bayan zaman sa ministan Ilimi a Abuja ranar Juma’a.
Mamman ya ce mutum 1,105 ke amfani da shaidar kammala digiri na boge daga kasar Togo.
” Akwai jami’o’i uku a kasar Togo da wasu guda 5 a Jamhuriyyar Benin, da sune muka sani sannan muka amince suna ba da shaidar kammala digiri na gaskiya.
Bayan haka Mamman ya ƙara da cewa a cikin shekara 1, ma’aikatar ilimi ta tarayya ta yi nasarar saka yaran da ba su zuwa makaranta akalla miliyan 4 makaranta.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
