Connect with us

News

Wani Matashi Ya Rasa Ransa A Hannun Ƴan Daba Bayan Sun Ƙwace Masa Waya A Kano 

Published

on

IMG 20240903 WA0001

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Matashin mai suna Bello Bello wanda akewa laƙabi da Khalifa ya rasa ransa ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata da misalin ƙarfe 9 na dare a unguwar yamadawa dake ɗorayi, bayan da ake zargin masu kwacen waya ne suka hallaka shi bayan sun karɓe wayar tasa.

Advertisement

Kwana guda da dawowarsa daga Jami’ar Ummaru Musa Ƴar Aduwa dake jihar Katsina, wanda daga bisani kuma aka garzaya dashi asibiti kafin ya ce ga garinku nan.

Innallahi Wa’innah Illaihi Raji’un Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Tsohon Shugaban Kasa Yar’adua Rasuwa

“Na kira shi a waya nake tambayar sa ko yana ina, ya ce dani mahaifiyarsa ce ta aikeshi ALKHAIRAT ya amso mata Memory, sai nace dashi to kafin yaje natan yazo ya ɗauki gawayin dana zo dashi ya kai gida, to bayan yazo ne kuma ya sameni a cikin wani Kemis a zaune nace dashi ga gawayin sai ya ɗauke shi zuwa gida. To bayan nazo gida ne kuma sai ban sameshi ba saboda ya tafi wajen da mahaifiyarsa ta tura shi sai kawai mukaji sallamar yara suna cewa gashi can an sari Khalifa.”Inji mahaifinsa

Advertisement

To sai dai kuma bayan an kaishi makabarta domin binne shi sai aka jiyo wasu matasa daga gefen maƙabartar suna yin wata magana ta cikin lasifika, wanda kuma wasu daga cikin al’ummar yankin sukai kan matasan har sukayi nasarar kama mutum biyu daga cikin su kamar yadda wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar INDA RANKA.

A zantawar Jaridar INDA RANKA da Tijjani Muhammad wanda shine shugaban ƴan Bijilanti na yankin yamadawa ya ce sun samu labarin abinda ke faruwa ne wanda kuma ba suyi wata-wata ba suka kai ɗauki wajen da matasan suka farwa waɗanda ake za gi da kunna lasifikar inda kuma suka kama mutum biyu daga cikin su.

Advertisement

Wanda kuma ya ce bayan sun kammala binciken su ne kuma suka miƙa su ga ofishin ƴansanda na yankin domin cigaba da binciken.

Idan dai za’a iya tunawa ko a ranar Alhamis da juma’ar da mukai bankwana da ita dai a cikin unguwar ta ɗorayi chiranchi an halaka wani matashi mai sana’ar sayar da ƙwai da kuma wani matashin mai sana’ar sa a bakin titin yankin kamar yadda Shugaban Babbar Kungiyar Tsaro ta yankin Ɗorayi Dakta Abdullahi Idris Muhammad Ɗan Fodiyo ya shaidawa Jaridar INDA RANKA.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending