Connect with us

News

Gwamnati Ta Sahalewa Ma’aikata Tsarin Yin Aiki Daga Gida

Published

on

FB IMG 1725533222413

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo Olu ya sahalewa ma’aikatan gwamnatin jihar damar yin aiki daga gida duba da tsadar rayuwa da ake ci gaba da fuskanta.

Advertisement

Tsarin na tsawon wata hudu masu zuwa ya fara aiki ne tun daga 4 ga Satumbar da muke ciki na bana.

Tsohon Shugaban Nigeriya Oleshegun Obasanjo Ya Zo Ta,aziyuar Mahaifiyar Umaru Musa Yar Aduwa

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar ta Lagos, Bode Agoro ya sanyawa hannu.

Advertisement

Idan ba a manta ba, tsarin yin aiki daga gidan ya fara aiki ne tun a watan 28 ga Fabrairun na bana, ta baiwa ma’aikatan dake matakin albashi na daya zuwa ma na sha hudu suyi aiki na kwana daya na kowane mako.

Hakan dai na zuwa ne a wani mataki na rage radadin cire tallafin mai da gwamnatin tarayya tayi akan ma’aikata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending