News
Gwmnatin Tinubu: Yan Boko Haram Ya Kamata A Kama Ba Masu Zanga_Zangar Tsadar Rayuwa Ba _ Atiku Abubakar
DAGA MAHAMMAD MAHAMMAD ZAHRADDIN
Tsohon mataimakin Shugaban kasar Nijeriya Kuma Jagoran babbar Jam’iyyar adawa ta PDP , Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa ya zargi Gwamnatin ƙasar nan da mayar da hankali kan wasu abubuwa da ya kira marasa muhimmanci tare da yin watsi da matsalar tsaro da ta addabi ƙasar musamman ma Yan Arewacin Najeriya.
wazirin Adamawa ya fadi haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zimunta na X Wanda akafisani Twitter inda, ya yi Allah wadai da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai Jihar Yobe, da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Ya kuma yi tsokaci kan yawan tashe-tashen hankula da ke ci gaba da faruwa a Jihohin Katsina Sokoto Zamfara Yobe Maiduguri da sauran sassan Arewa.
Atiku ya zargi Gwamnati da cewa ta fi damuwa da kama masu zanga-zangar tsadar Rayuw maimakon magance matsalar rashin tsaro.
Duk da mummunan zubar da jini da aka yi a Yobe, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da kuma ɓarnar da aka yi a ƙauyuka da dama a Katsina da Sakoto, da sauran a garuruwan da ke yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, ga dukkan alamu Gwamnati ta fi mayar da hankali kan ayyukanta da sauran abubuwa da ba su da muhimmanci.” in ji Atiku.
