News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Cazar Naira 50 A Kan Hada-hadar Kudin Da Ta Kai Naira Dubu 10 A Opay
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Cazar Naira 50 A Kan Hada-hadar Kudin Da Ta Kai Naira Dubu 10 A Opay
Kamfanin Opay ya sanar da wannan mataki zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Satumba, 2024.
Bisa umarnin hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya kamfanin yace kwastomomi za su fara biyan N50 a duk lokacin da sukayi hada-hadar kudin da ta kai N10,000 zuwa sama.
Ba Huruminmu Ba Ne Samar Da Gurbin Neman Shiga HND –Hukumar JAMB
Ƙaddamar da wannan kuɗin ya biyo bayan ƙoƙarin gwamnatin tarayya na samar da kudaden shiga daga hada-hadar lantarki ta hanyar dokokin FIRS.