News
Ba Huruminmu Ba Ne Samar Da Gurbin Neman Shiga HND –Hukumar JAMB
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa JAMB ta yi Allah-wadai da iƙirarin da ake na cewa tana da hannu a cikin shirin ɗaukar ɗalibai masu babbar difiloma wato HND.
A wata sanarwa da kakakin hukumar JAMB Fabian Benjamin ya sanya wa hannu, ya ce hukumar ba ta da hannu, ko iko, ko kuma ta gudanar da ayyukan shigar da masu babbar difiloma HND.
Kowa Na Da Damar Sayen Mai A Matatar Dangote — Kamfanin NNPC
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta JAMB ita ma ba ta da alhakin sauran shirye-shiryen manyan makarantu baya ga shigar da su a kai a kai.
Hukumar ta kuma ƙara da cewa ba ta san masu neman shiga HND ba kuma ba su da alaƙa da aikin JAMB.
A baya dai wasu ɗaliban HND sun zargi hukumar da laifin rashin zuwa yi musu hidimar bautar ƙasa wato NYSC.
Jaridar BLUEPRINT NEWSPAPER ta ruwaito cewa wasu ɗaliban sun yi iƙirarin cewa ba a tara su aikin yi ba ne saboda sun yi wani shirin na wucin gadi na kamm