Connect with us

News

Mun Samu Nasarori Daga Fara Gudanar Da Aikin Mu Zuwa Yau. Wajen Daƙile Faɗan Daba Da Ƙwacen Waya — KOSSAP

Published

on

IMG 20240909 WA0003

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

Shugaban Rundunar Tsaro mai yaƙi da faɗan daba, da kuma daƙile kwacen waya, da magance harkokin Shaye-Shaye, a jihar  Kano, kuma mashawarci na musamman ga Gwamnan Kano akan harkokin tsaro ANTI PHONES SNATCHING (KOSSAP) ya ce  sun samu nasarori daga fara gudanar Da aikin mu zuwa yau wajen daƙile faɗan daba da ƙwacen waya a jihar.

Advertisement

Inuwa Salisu Sharaɗa ya bayyana hakan ne yayin da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network ta ƙasa, ta kai ziyara ta musamman a ofishin rundunar da yammacin Lahadin nan.

Da yake nasa jawabin babban jami’in gudanarwar ƙungiyar a matakin ƙasa Tasi’u Idris Idris (Soja) ya ce sun kai wa jami’an rundunar ziyarar ne domin yaba musu bisa yadda suke ƙoƙari wajen kakkaɓe ɓata gari, har ma ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta wadata su da kayan aiki duba da ƙalubalen ƙarancin kayan aiki da motoci da suke fuskanta.

Advertisement

Jaridar INDARANKA ta ruwaito cewa a yanzu haka suna da babura masu ƙafa biyu da kuma adaidata sahun da suka kamo daga wajen ɓarayi wanda a yanzu haka suke hannunsu kuma da zarar sun kammala bincike zasu miƙa su ga hukuma domin ta ɗora sai kuma a gurfanar dasu a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.

“Daga lokacin da Gwamnan Kano ya rantsar damu mun samu nasarori mabanbanta da suka haɗar da samun Nasara kan masu kwacen wayoyi da masu faɗan daba harda sulhunta tsakanin iyayen da ƴaƴansu suka gallabesu da dai sauransu ayyuka.”Inji shi.

Advertisement

Ya kuma bayyana irin ƙalubalen da suke fuskanta baya wuce samar musu da wadatattun kayan aiki da suka haɗar da motoci domin fita aiki da kuma basu dama domin ƙaro musu ma’aikata ta yadda aikin nasu zai ƙara ƙarfafa.

Sannan ya shaidawa jaridar Indaranka cewa babban ƙalubalen da mukafi fuskanta shine

Advertisement

“yadda muke ƙoƙarin kama masu laifi amma muna samun wasu daga cikin jami’an tsaro Masu ɗamara suna karɓarsu wanda hakan ke dawo mana da aikinmu baya.”

Ya kuma ja hankalin al’umma da suke basu gudunmuwa musamman ma idan sun samu mai laifi da su ke tuntuɓarsu domin kawo musu agajin gaggawa.

Advertisement

Wannan dai na zuwa ne bayan wani taron manema labarai da rundunar tayi a yammacin wannan ranan domin sanarwa da al’umma irin aikace-aikacen da suke yi da kuma yunƙurinsu na ganin sun mai da jahar Kano tsaftatacciya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending