News
DA DUMI DUMI : Gwamnatin Jihar Kano Ta Ayyana Ranar Bikin Hutun Takutaha
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 23 ga watan Satumba a matsayin ranar hutun bikin Takutaha.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun, babban sakataren Gwamnatin Abba Danguguwa da shugaban ma’aikatan gwamnati, ta ce za’ayi taron ne domin tunawa da ranar 7 ga wata domin maulidin manzon Allah.
Ya ce Jama’ar Kano na murnar ranar a dukkanin irin wannan rana ta Takutaha.
Takutaha, wani biki ne na tarihi da aka yi shi tsawon shekaru aru-aru domin tunawa da ranar da akayi suanan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam S A W.
Nigerian Tracker
Advertisements
