News
Iran ta harba ɗaruruwan makamai masu linzami cikin Isra’ila
DAAG YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Isra’ila ta sanar da rufe sararin samaniyar ƙasar, tana karkatar da jirage zuwa wasu filayen jiragen na ƙasashen waje a cewar kafar yada labaran Isra’ilan Sanarwar na zuwa ne bayan da Iran ta harba makamai masu linzami sama da 100 cikin Isra’ila.
Idan har gwamnatin masu tsananin aƙidar kafa ƙasar Isra’ila ta mayar da martani kan ayyukan Iran, to za ta fuskanci munanan hare-hare – in ji Dakarun kare juyin juya hali na Musulunci na Iran.
DA DUMI-DUMI: Iran Ta Fara Harba Makamai Masu Linzami Masu Tarin Yawa Cikin Isra’ila
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Turkiyya Anadolu Agency ya rawaito cewa an ga makamai masu linzami da yawa a samaniyar Gabar Yammacin Kogin Jordan suna fitowa daga gabas zuwa Negev na Tel Aviv.