Connect with us

News

FAƊAWA A KOGI : Colorado Ta yi Sanadiyyar Mutuwar Wani  Mutum

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Rundunar ƴan sandan Jihar Legas ta tabbatar da cewa, wani mutum ya kashe kansa ta hanyar faɗawa a kogi sakamakon tasirin shan miyagun ƙwayoyi da ake kira da ‘Colorado’.

Kakakin rundunar na jihar, SP Benjamin Hundeyin ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aika wa da Jaridar BLUEPRINT.

Tsadar Wake Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana’ar Kosai A Kano

Ya ce lamarin ya auku ne a ranar 11 ga watan Oktoba, 2024 inda wani mutum ɗan shekara 45 mai suna Kazeem ya sheƙa a guje tare da faɗawa cikin wani babban rafi da ake kira Odo Tente wanda ke kan iyaka na tsakanin jihohin Legas da Ogun.

Faruwar hakan ke da wuya, mutumin ya mutu sakamakon zargin Colorado da ake ganin ita ce musabbabin mutuwar tasa.

Tuni dai jami’ai suka ziyarci inda lamarin ya auku tare da ɗaukar hotuna inda a nan aka kira mahaifin mamacin tare da sanar da shi wanda ya ce a binne shi a nan kusa da rafin kamar yadda al’adar su ta tanadar.

Advertisement

Kawo yanzu dai ana gudanar da bincike game da ababen da ke da alaƙa da mutuwar mamacin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending