Connect with us

News

Muhimmin Sako Zuwa Ga Al’ummar Annabi Muhammad (SAW)— Daga Imam Murtadha Gusau

Published

on

Muhimmin Sako Zuwa Ga Al'ummar Annabi Muhammad (SAW)!

 

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

 

Assalamu alaikum

 

Tabbas, ko shakka babu a kasar nan da kuma jihohin mu, muna cikin matsaloli masu tarin yawa, wadanda ba sai an yi ta wani dogon bayani a kan su ba. Yawaita surutai akan matsaloli ba shi muke nema a yau ba. Abun da muke bukata shine, kokarin lalubo hanyar magance wadannan matsaloli da suka dabaibaye mu.

Advertisement

 

Wurin samo wannan mafita, ba bangare guda zamu yi ta kallo ko kokarin dora wa laifi ba, a’a, sai mun hada hannu, mun hada karfi da karfe, kowa ya kawo irin gudummawa da Allah ya hore masa, domin ganin an kai ga inda ake so akai.

 

Kowanen mu yana ta fadar albarkacin bakin sa a kan mafita akan matsalolin mu. Masu zagi nayi, masu cin mutunci suna yi, masu karya da kage da sharri da zarge-zarge duk suna yi. Kai da ma abunda ban ambata ba, kowa da irin abunda ya dauka, wai da nufin shi yana ganin wannan, zai iya zama mafita daga matsalolin mu.

Amma a gaskiya, ni ina da sabani da duk wadannan mutane. Domin ni nayi imani da maganar Allah Subhanahu wa Ta’ala da Manzonsa (SAW) dari-bisa-dari cewa, matsalar nan tamu ce dukkanin mu. Mune muka jawo ta. Mune ummul haba’is na afkawa cikin wadannan duk fitintinu. Sannan kuma gyaran yana hannun mu, idan mun neme shi a wurin Allah Mahaliccin mu.

Farashin Gas Din Girki Ya Haura Zuwa Naira 1,500 Duk Kilo

Eh, hakika, gyara yana hannun Allah, shine mai gyarawa, amma da sharadin cewa, sai idan mun nemi gyaran da gaske, sannan Allah yasa muna hannu ya gyara muna.

Advertisement

 

Lallai tabbas, hakika duk wanda ya bibiyi wadannan Hadisai na Manzon Allah (SAW), ya karanta su, yayi nazari a kan su, ya fahimce su, ya karanta sharhi da bayanan malamai a kan su, to tabbas, hakika, zai ga cewa Annabi (SAW) ya fada muna cututtukan da zasu afkawa wannan al’ummah tasa; ya fada muna dalilan da zasu jawo wadannan cututtuka su afka masu, da kuma hanyoyin magance su. Don haka, lamarin ba surutu bane, ba hayaniya bane, ba zage-zage ko cin mutuncin wani ko wasu bane, sannan ba kuma wani zafin kai ko wata hamasa bane.

 

Mun san tarihin mu, mun san illolin mu, mun san yadda muke a da, mun san abubuwan da suka zama sanadiyyar afkawar mu cikin wannan masifa da bala’i, mun san cutar mu, kuma mun san maganin. Don haka ya rage namu. Muje zuwa mu gani, idan dai har hayaniya, da kumfar baki, da tashin hankali, da zage-zage, da cin mutunci, da hamasa, da zafin kai, da rashin kunya, da aikin jahilci, idan zasu iya gyara muna halin da muka samu kan mu a ciki.

 

عن ابن عمر -رضي الله عنهما – قال: سمعت رسول الله ﷺ يقول: “إذا تبايعتم بالعينة وأخذتم أذناب البقر ورضيتم بالزرع وتركتم الجهاد سلط الله عليكم ذلا لا ينزعه شيء حتى ترجعوا إلى دينكم.” [رواه أحمد وأبو داود]

Advertisement

 

يُوشِكُ أن تَدَاعَى عليكم الأممُ من كلِّ أُفُقٍ، كما تَدَاعَى الْأَكَلَةُ إلى قَصْعَتِها، قيل: يا رسولَ اللهِ! فمِن قِلَّةٍ يَوْمَئِذٍ؟ قال لا، ولكنكم غُثاءٌ كغُثاءِ السَّيْلِ، يُجْعَلُ الْوَهَنُ في قلوبِكم، ويُنْزَعُ الرُّعْبُ من قلوبِ عَدُوِّكم؛ لِحُبِّكُمُ الدنيا وكَرَاهِيَتِكُم الموتَ.”

 

الراوي: ثوبان مولى رسول الله صلى الله عليه وسلم | المحدث: الألباني | المصدر: صحيح الجامع | الصفحة أو الرقم: 8183 | خلاصة حكم المحدث: صحيح.

 

يُوشِكُ الأممُ أن تداعَى عليكم كما تداعَى الأكَلةُ إلى قصعتِها. فقال قائلٌ: ومن قلَّةٍ نحن يومئذٍ؟ قال: بل أنتم يومئذٍ كثيرٌ، ولكنَّكم غُثاءٌ كغُثاءِ السَّيلِ، ولينزِعنَّ اللهُ من صدورِ عدوِّكم المهابةَ منكم، وليقذِفَنَّ اللهُ في قلوبِكم الوهْنَ. فقال قائلٌ: يا رسولَ اللهِ ! وما الوهْنُ؟ قال: حُبُّ الدُّنيا وكراهيةُ الموتِ.”

Advertisement

 

الراوي: ثوبان مولى رسول الله صلى الله عليه وسلم | المحدث: الألباني | المصدر: صحيح أبي داود

الصفحة أو الرقم: 4297 | خلاصة حكم المحدث: صحيح.

 

عن العِرْباضِ بن ساريةَ رضي الله عنه قال: قام فينا رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم، فوَعَظَنا مَوعظةً بليغةً وَجِلتْ منها القلوبُ، وذَرَفتْ منها العيونُ، فقيل: يا رسول الله، وعظتَنَا موعظةَ مُودِّعٍ فاعهد إلينا بعهد. فقال: “عليكم بتقوى الله، والسمع والطاعة، وإن عبدًا حبشيًّا، وسترون من بعدي اختلافًا شديدًا، فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين، عَضُّوا عليها بالنواجِذ، وإياكم والأمور المحدثات، فإن كل بدعة ضلالة.”

[صحيح – رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد – سنن ابن ماجه – 42]

Advertisement

 

Idan mun kalli yadda wadannan Hadisai suka lissafo matsalolin, zamu kalle su kamar haka:

 

1. Yawaitar Cin Riba a cikin al’ummah. Da sharri da cuta da cin amana da magudi da makirci da cin haramun a cikin kasuwancin mu. Da kokarin tara abun duniya da dukiya ta ko wace hanya, wanda ko shakka babu, yawancin ‘yan kasuwar mu sun yi nisa a cikin wadannan bala’o’a, sai fa ‘yan kadan daga cikinsu, wadanda Allah ya kare.

 

2. Guje wa addinin Allah, kin taimaka masa; wulakanta ilimin addini da fifita ilimin boko a kan sa. Kin bayar da muhimmanci wurin neman ilimin addini. Fifita duk wani abu da ya shafi ilimin boko, da rainawa da wulakanta duk wani abu da ya shafi ilimin addini.

Advertisement

 

3. Barin yin gwagwarmaya ta gaskiya, ta tsakani da Allah, domin ciyar da addinin Allah gaba.

 

4. Yin amfani da addini domin tara abun duniya. Ko kuma yin amfani da addini domin cimma wata gurbatacciyar manufa. Shiga cikin riga ko inuwa ko rumfar addini ana yaudarar al’ummar Annabi Muhammad (SAW).

 

5. Matsanancin son duniya da kuma tsananin ki ko gudun lahira, alhali Allah ya fada muna lahira ita ce mafi alkhairi.

Advertisement

 

6. Tsoron mutuwa, ko tsoron yin bakin jini wurin fadar gaskiya, da jin cewa dole sai an faranta ran wasu ko wani.

 

7. Tsoron Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi karanci a cikin wannan al’ummah ta Annabi Muhammad (SAW).

 

8. Rashin yin da’a da biyayya ga shugabanni yayi karanci a cikin wannan al’ummah ta Annabi Muhammad (SAW).

Advertisement

 

9. Rashin mutunta sabani da ra’ayoyin junan mu.

 

10. Kauracewa Sunnah da tafarkin Manzon Allah (SAW), da bin wasu hanyoyi wadanda ba ita ba.

 

11. Kauracewa tafarkin magabatan mu na kwarai, shiryayyu masu shiryarwa.

Advertisement

 

12. Afkawa cikin bidi’o’i da barna da bata da shirka da kafirci da tsafe-tsafe da halaka, da badala iri-iri. Kiri-kiri, muna ji muna gani, don jahilci, ko son zuciya, ko son abun duniya.

 

13. Kauracewa duk wasu makarimul akhlaq, da dabi’u da halaye na kwarai, halaye nagari, wadanda muka gada a cikin addinin mu, da kuma wurin iyayen mu da kakannin mu da dukkan magabatan mu.

 

Kuma da ikon Allah, mafita daga duk wani mummunan kangi da muka fada shine, komawa akan addinin Allah da gaske, tare da komawa akan tafarkin da magabatan mu suka bi suka ci nasara. Tare da kuma sanya tsoron Allah Subhanahu wa Ta’ala a cikin dukkanin huldodin mu, na addini da na rayuwa. Da kokarin kamanta gaskiya da rikon amana da kwatanta adalci a cikin dukkan abunda zamu yi.

Advertisement

 

Ko shakka bana yi, idan munyi wannan, da yardar Allah, zamu sha mamaki, zamu ga irin yadda Allah zai yi ikon sa.

 

Amma duk wani rudu, da wata hayaniya, da wasu surutai, da wani zarge-zarge ko zage-zage ko batanci ko cin mutunci ko wani tayar da jijiyar wuya, ko zargin wani ko wasu, ko yiwa wani karya, ko wani karyar ilimi, wallahi duk ba zai fitar da mu ba.

 

Mafitar dai, duk tana wurin Allah, amma sai mun nema da gaske, sai mun bi hanyar da ya dace, sai mun yi abunda ya kamata, sai mun nuna da gaske muke yi, sai mun cire duk wani munafurci a tattare da mu, sannan zamu ci nasara da izinin Allah Subhanahu wa Ta’ala.

Advertisement

 

Idan mun shekara miliyan muna ta koke-koke da korafe-korafe, matukar bamu bi hanyoyin da suka dace ba, to a haka zamu kare a banza, ba tare da cimma wata ingantacciyar nasara akan abun da muke so ba.

 

Domin baya yiwuwa kace kana son gyara, amma kuma kaki bin hanyoyin da suka dace. Ko kuma kai ma kabi son zuciya wurin kawo gyaran. Shi yasa, gamu nan, kullum muna ta fadi-tashi akan matsalolin mu, amma sai Allah ya hana muna cin nasara, saboda mun ki bin hanyoyin da suka dace.

 

Kuma mun sani, samun gyara kuwa, baya yiwuwa da bin son zuciya!

Advertisement

 

Allah yasa mu gane, Allah ya taimake mu, yayi riko da hannayen mu, da na shugabannin mu, ya tausaya muna, ya gyara muna kasar mu da jihohin mu, amin.

 

Wassalamu alaikum,

 

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending