Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Ta  Buƙaci Mutane Su Fito Domin Ayimusu Gwajin Hawan Jini da Ciwon Siga

Published

on

IMG 20241031 WA0036

 

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Advertisement

Yayin da aka fara aiwatar da Shirin Gangamin Mutane Miliyan Goma a faɗin wannan ƙasa, an buƙaci al’ummar jihar Kano da su fito domin yi musu gwajin hawan jini da ciwon siga.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan kira a ranar Litinin da ta gabata yayin fara aiwatar da shirin a harabar Hukumar Samar da Magunguna da Kayayyaki ta Jiha (DMCSA).

Advertisement

Shirin Gangamin Mutane Miliyan Goma ya mayar da hankali ne ga cututtuka marasa yaɗuwa, musamman hawan jini da ciwon siga, waɗanda ke taka rawa sosai wajen haifar da cututtuka da mace-mace a Najeriya, da ya sanya Zauren Kwamishinonin Lafiya na Najeriya ya ɗamfaru da shirin wajen magance matsalar, wanda gangami ne na ƙasa baki ɗaya da ke da ƙudirin yi wa ‘yan Najeriya miliyan goma gwajin hawan jini da ciwon siga a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya na Abuja, a tsawon mako guda.

Daga cikin manufofin shirin akwai yi wa al’ummar Najeriya miliyan goma gwajin hawan jini da ciwon siga, da haɗa sakamakon da aka tabbatar da hanyoyin samun waraka, da samar da magunguna na ƙaramin zango daidai da tsarin da ya dace, da ƙara wayar da kan al’umma da ilimantar da su game da hawan jini da ciwon siga, da ilimantar da al’umma game da abincin da za su rinƙa ci, da motsa jiki, da kaucewa shan taba, da sauransu.

Advertisement

Dakta Labaran ya buƙaci mutane da su shigo a dama da su a cikin wannan aiki don tabbatar da yadda matakin lafiyarsu yake, ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da waɗannan cututtuka za a ba su magani kyauta ko kuma a tura su asibiti mafi kusa domin a ci gaba da kula da lafiyarsu idan an fahimci larurar tasa babba ce.

Kwamishinan ya shawarci jama’a da su kai iyalansu wuraren da aka ware don yin gwajin a cibiyoyin da aka tanada don yin aikin kyauta har tsawon mako guda a faɗin jihar Kano, yana mai fatan yi wa mutane miliyan ɗaya a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Advertisement

Ya ce “Aikin, wanda zai lashe kusan Naira miliyan 800, babba ne. Saboda haka, mutane, daga kan ɗan shekara 20 zuwa sama, na buƙatar su yi cikakken amfani da wannan dama wajen yin gwajin waɗannan cututtuka masu hallakarwa. Waɗanda aka samu da ɗaya ko kuma duka cututtukan kada su razana, maimakon haka su gode wa Allah saboda an gano wata cuta da ta ɓuya a jikinsu, domin su nemi waraka.

Dakta Labaran ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake nuna damuwa da lafiyar al’ummar jihar Kano a kowane lokaci, ya kuma jinjina wa ƙungiyoyi masu tallafa wa fannin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suke bayar da gudummawa wajen ci gaban lafiya.

Advertisement

Sa hannu:
*Ibrahim Abdullahi*
Jamiin Yada Labarai
Maikatar Lafiya
30 ga Oktoba 2024

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending