News
Wasu ‘Yan Kasuwa Sun Koka Kan Halin Da Suke Ciki Na Yunkurin Sabunta Kasuwar Mile 12
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu Yan Kasuwar Mile 12 dake Jihar Lagos da suka fito daga Jihohin Arewa Dan sauran sassan Najeriya sun koka da halin da suka samu kansu a Kasuwar Mile 12 dake Jihar Lagos.
Sun zargi cewa Gwamnatin Jihar Lagos a yunkurinta na sabunta Kasuwar ta samar da wani Dan Kwangila da zai aikin, sannan Yan Kasuwar zasu sake biyan wasu kudade gareshi duk da cewa Shagunan Mallakinsu ne da suka siya daga Gwamnati tun Asali Kamar yanda Arewa Radiyo ta ruwaito.
Yawan Shan Sukari Ga Kananan Yara Na Haifar Da Cutar Suga Idan Aka Girma —Bincike
Yan Kasuwar sun bukaci Gwamnatin data Basu tabbacin ba tashinsu zasuyi daga Kasuwar ba bayan an gama Sabuntata. Tare da bukatar da Manyan Kasuwar ta Mile 12 da suyi musu cikakken bayani kan yadda ake tasrifi da kudin shiga na Kasuwar da aka dade ana Tarawa.
Sun bayyana cewa kudaden da akasa kan kowanne Shago da za a sake ginawa ya kai kimanin Naira Miliyan 5 Wanda hakan kuma yayi musu tsada a cewar wasu ‘yan Kasuwar.
