News
Yawan Shan Sukari Ga Kananan Yara Na Haifar Da Cutar Suga Idan Aka Girma —Bincike
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani bincike ya nuna cewa san suga da yawa a lokacin yarinta da ma lokacin da yaro ke ciki na haifar da yuwuwar kamuwa da cutar suga da hawan jini bayan mutum ya girma.
Wannan na cikin wani rubuta da aka wallafa a mujallar lafiya ta Nature a ranar Alhamis kamar yanda Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito
Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje 130 Da Ake Zargi Da Sata Ta Yanar Gizo
Binciken wanda wani masanin tatalin arziƙi ya jgoranta mai Tadeja Gračner na jami’ar Kudancin California a Los Angeles, ya fitar da wasu bayanai da ya tattaro daga matattarar adana bayanai ta ƙasar Ingila cewa mutanen da suke shan suga kaɗan a shekarun 1950, suna da kaso 36% na yuwawar kamuwa da cutar suga da kaso 20% na kamuwa da hawan jini idan aka kwatanta da sauran mutane.
Binciken ya nuna cewa shekarun da suka fi haɗari na yarinta su ne daga wata shida zuwa shekara biyu a lokacin da nau’in abincin da mutum ke ci ke da matukar tasiri bayan girma.
“Yawan sugan da yaro ke sha daga lokacin da ya cika wata shida na da tasiri ga yuwuwar kamuwa da cutattuka a rayuwarsa ta gaba. Haka waɗanda iyayensu suka riƙa ɗura musu suga a lokacin da suke ciki. Su ma akwai yuwuwar su kamu da cutar suga da hawan jini idan aka kwatanta da waɗanda ba su sha suga da yawa ba,” a cewar rahoton.
Haka zalika a cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO) da ƙungiyar kula da larurar cutar sukari ta duniya (IDF), sun ce kusan manyan mutane miliyan 537 ke fama da cutar , wato kaso 9.3 kenan na yawan al’ummar duniya (ƙididdigar 2021).
Hakan na nufin a duk mutane biyar, ɗaya yana ɗauke da cutar suga da kuma yake neman magani. Sannan ana hasashen cewa mutanen da zu gamu da cutar sukari za su iya kai wa miliyan 784 zuwa nan da 2045.
Yankin da ta fi kowacce yawan masu cutar suga ita ce Arewacin Amurka da ke da kaso 14.3%, sai Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka masu kaso 13.7 da Kudancin Asiya mai kaso 11.7.
