Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje 130 Da Ake Zargi Da Sata Ta Yanar Gizo

Published

on

Ƴansanda Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje 130, Da Ake Zargi Da Sata Ta Yanar Gizo

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya (NPF) ta kama mutane 130, ciki har da ‘yan ƙasar waje 113 – galibinsu ‘yan ƙasar Sin da Malaysiya – da kuma ‘yan Nijeriya 17 bisa zargin yin sata ta yanar gizo da wasu ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Advertisement

Mutanen sun haɗa da maza 87 ‘yan ƙasar waje da mata 26, tare da maza huɗu da mata 13 ‘yan Nijeriya, aka kama su a wani sumamen da aka kai kan wasu ayyukan sata ta yanar gizo.

Jariri Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hatsarin Mota Da Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 10

A cewar ACP Olumuyiwa Adejobi, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, an gudanar da sumamen ne a yau 3 ga Nuwamba, 2024, a wani gini kusa da Next Cash and Carry a Jahi, Abuja.

Advertisement

AIG Benneth Igweh na shiyya ta 7 ne ya jagoranci aikin tare da haɗin gwuiwar cibiyar yaki da laifukan yanar gizo ta ƙasa (NPF-NCCC), inda suka ƙwace kwamfutoci da wasu na’urori masu da ake amfani da su wajen aikata laifin.

 

Advertisement

 

LEADERSHIP HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending