Hukumar kare bayanan mutane ta kasar Kenya ta ci tarar wata makaranta dala 31,000 saboda wallafa hotunan dalibanta a yanar gizo ba tare da izinin iyayensu ba.
Wannan ne mataki irinsa na farko da sabon ofishin kare bayanan mutane ya dauka.
Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari A Kaduna Sun Kashe Mutum 6
Haka zalika, hukumar ta ci tarar wani gidan rawa dala 12,000 da kuma wani kamfanin ba da bashi dala 20,000.
A cewar hukumar, gidan rawar ya buga hoton abokin huldarsa a shafinsa na sada zumunta, ba tare da izini ba.
Shi kuma kamfanin ba da bashin ya rika yi wa abokan huldarsa barazana ta hanyar kiraye-kirayen waya da aika sakonni daga bayanan da ya samu ta wasu hanyoyi daban.
Tarar ta janyo muhawara game da ‘yancin tsare sirrin mutane musamman a gidajen rawa da na shan barasa.
Wasu cikin irin wadannan cibiyoyi a yanzu sun fara wallafa sanarwar cewa duk mutumin da ya sa kafa ya shiga harabobinsu, tamkar ya yarda ne a dauki hoto ko bidiyonsa ba tare da neman diyya ba, kuma duk wanda bai yarda da dokokinsu ba, to kada ya shiga.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin X, ta ce tana fata tarar da ta ci cibiyoyin za ta aika wani sako ga ire-irensu a kan su rika bin dokokin kare bayanan mutane na kasar ciki har da wadanda suka bukaci a nemi amincewar mutum kafin a buga hotunansu a intanet.
wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari A Kaduna Sun Kashe Mutum 6
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta soke Nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben 2023, inda ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Tunda farko, hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ayyana Yusuf wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar NNPPa matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai Jam’iyyar APC ta garzaya gaban Kotu
A biyo mu domin karin bayani nan gaba.