Connect with us

News

Akwai Yiwuwar Ta Yanar Gizo Za A Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wata kwakkwarar majiyar tsaro ta shaida wa jaridar Aminiya a Kotun da za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano cewa har yanzu ba su san inda alkalan kotun suke ba, kuma da alamar ba za zo zaman da kansu ba.

Majiyar ta ce akwai yiwuwar alkalan za su halarci zaman ne ta bidiyo ta yanar gizo su kuma yanke hukunci, bisa umarnin da suka samu daga sama, saboda wasu dalilai na tsaro.

 

Ƴan sanda sun kori ƴan jarida daga kotu duk da sammakon da sukayi tun karfe 5 na Asuba.

Hakan na zuwa ne a yayin da ake yi ta tayar da jijiyar wuya a harabar kotun, bayan jami’an tsaro sun shaida wa bangarorin da ke shari’ar cewa mutum 50 kacal, ciki har da su da ‘yan jarida da lauyoyi kadai aka amince su shiga cikin kotun.

Advertisement

Jatidar Inda Ranka ta kawo rahoton yadda aka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da kewaye domin tabbatar da doka da oda.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending