Connect with us

News

Yan Arewa Basa Kalubalantar Dokar Ƙarin Haraji Da Shugaba Tinubu Zai Yi —Abdulmumin Kofa

Published

on

Yan Arewa Basa Kalubalantar Dokar Ƙarin Haraji Da Shugaba Tinubu Zai YiAbdulmumin Kofa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananun hukumomin Kiru da Bebeji, dake jihar Kano, Abdulmumin Jibril Kofa, ya bayyana kwarin gwuiwar sa akan cewa majalisar zata amince da kudirin kara harajin da shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ke neman yiwa yan Najeriya.

Advertisement

Sabuwar dokar harajin da shugaban Tinubu ke nema majalisa ta amince masa, ta samu kalubalanta daga bangaren al’ummar Arewacin Najeriya, har ma da majalisar tattalin arziki ta kasa inda ta nemi a dakatar da aiwatar da dokar.

Mahaifin Da Ake Zargin Ya Kashe Jiririnsa Ɗan Kwana 3 Ya Shiga Hannun Ƴansanda

Sai dai lokacin da ake zantawa da Abdulmumin Jibril Kofa, a kafar Channels tv, ya ce yan Arewa basa kalubalantar dokar.

Advertisement

Sannan ya nuna kwarin gwiwa akan cewa za’a amincewa dokar karin harajin, inda ya ce dokar zata Kawo wa Najeriya cigaba.

Shima a nasa bangaren shugaban Tinubu, ya ce ba zai janye kudurin daya dauka na aiwatar da garambawul a fannin karbar haraji ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending