Connect with us

News

An Yi Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da Tawagar Dan Ta’adda Bello Turji

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD TUKUNTAWA

Rahotanni na nuni da cewa  an yi musayar wuta na dogon lokaci tsakanin sojoji da tawagar ‘dan ta’adda Bello Turji a Gatawa dake Jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce tun karfe 6 na safe ake jin aman wuta a garin har zuwa kusan karfe 3 na ranar yau.

Tankar Dakon Mai Kife Tare Da Kamawa Da Wuta A Kano

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar DAILY TRUST cewar basu taba ganin irin wannan musayar wutar ba, kuma har zuwa lokacin da yake magana ana ta artabu tsakanin bangarorin biyu.

Ko a karshen mako sanda sabon shugaban rundunar Sojoji kasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya ziyarci yankin inda ya tattauna da dakarun dake aikin tabbatar da tsaro a Tangaza da Ilela a kan muhimmancin murkushe duk wani ɗan ta’adda cikin su harda Bello Turji.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending