News
Tankar Dakon Mai Kife Tare Da Kamawa Da Wuta A Kano
DAGA SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wata tankar dakon mai ta kife kuma ta kama wuta a kauyen Tsaida da ke kan hanyar Gaya zuwa Dutse a karamar hukumar Gaya a dake Kano.
Rahotanni na nuni da cewa ba a sami rahoton asarar rai ba.
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Goyon Bayansa Na Samar Da Halastacciyar Ƙasar Falasɗinu
Hakimin Kauyen na Tsaida, Aliyu Adamu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sakon murya, inda ya bayyana cewa tankar ta fadi da sanyin safiyar ranar, duk da cewa har yanzu ba a san musabbabin hadarin ba.
Haka zalika Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faduwar wata tankar dakon Mai tare da kamawa da wuta a yankin Tsaida da ke karamar hukumar Gaya.
Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na wannan rana, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar wa Dala FM.
Ya ce, tuni aka tura jami’an kwana-kwana daga ƙaramar hukumar Wudil, domin kai ɗaukin gaggawa.
