News
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Goyon Bayansa Na Samar Da Halastacciyar Ƙasar Falasɗinu
DAGA YASOR SANI ABDULLAHI
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun shugabannin ƙasashe wajen Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan Falasɗinawa a Gaza, sannan kuma ya bayyana goyon bayansa ga fatan samar da halastacciyar ƙasar Falasɗinu.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin taron ƙungiyar ƙasashen musulmi ta OIC da takwararta ta ƙasashen Larabawa Arab League, da aka gudana a birnin Riyadh fadar gwamnatin Saudiya.
DA DUMI-DUMI: An Samu Fashewar Wani Abu Mai Karfin Gaske A Jos
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen hulda da kafafen yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaba Tinubu na da yakinin cewa samar da halastacciyar ƙasar Falasɗinu ce kadai hanyar kawo ƙarshen rikicin.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci ɓangarorin da ke rikici da juya a yankin Gabas ta Tsakiya, su mutunta dokokin kare hakkin dan adam, kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.
Tunda farko a jawabinsa, yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed Bin Salman ya buƙaci tsagaita wuta a hare-hare da Isra’ila ke kaiwa Gaza da Lebanon, tsagaita wutar da jagoran ya kira na wajibi duba da halin da al’ummomin yankunan biyu ke ciki.
Bin Salman ya kuma bukaci bayar da damar shigar da dukkanin kayakin jinkai a Gaza, bisa la’akarin da yadda al’ummar yankin ke cikin mawuyacin hali.
