News
DA DUMI-DUMI: An Samu Fashewar Wani Abu Mai Karfin Gaske A Jos
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An samu fashewar wani abu mai karfin gaske a birnin Jos, babban birnin jihar Filato a safiyar ranar Talata a wani wuri kusa da yankin kasuwar Terminus mai yawan jama’a.
Wata majiya daga garin ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa a halin yanzu jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, jami’an kashe gobara, da tawagar motocin daukar marasa lafiya na can a wurin da lamarin ya faru domin kai dauki.
Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata ba tare da tabbatar da asarar rayuka da yawan barnar da aka yi ba.
Majiyar ta kara bayyanawa PUNCH cewa mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar bam din, inda wasu majiyoyi ke nuni da cewa an samu asarar rayuka.
Wasu majiyoyin tsaro a hedikwatar ‘yan sandan da ke Jos ma sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka kara da cewa an fara gudanar da bincike.
