News
Kungiyar Manyan Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi A Najeriya
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kungiyar manyan likitoci tare da likitocin hakora sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai daga ranar Litinin dinnan a Najeriya
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewe lamarin da ake fargabar zai iya janyo tsayawar aiki a kusan cibiyoyin kiwon lafiya 83, da kuma makarantun kiwon lafiya 64 a fadin kasar, kamar yadda shugaban kungiyar na kasa Farfesa Muhammad Muhammad wanda ya bayyana a wata tattaunawa
A cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, ta ayyana cewa za ta shiga yajin aikin gargadi ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kungiyar.
Yajin aikin ya soma a dukkan jami’o’i da manyan asibitocin Nijeriya daga Litinin 17 ga wata, zuwa Lahadi 24 ga watan Nuwamba, 20
24.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
