News
Olusegun Obasanjo Ya Nemi A Kori Shugaban Hukumar INEC Da Wasu Jami’ain Hukumar.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi kira da a yi wa tsarin zaben ƙasar garambawul, inda ya ce akwai buƙatar a kori shugaban Hukumar Zaɓen Ƙasar INEC Mahmood Yakubu da wasu jami’ain hukumar.
A jawabin da ya yi a yayin taron shugabanci na Chinua Achebe, da ya gudana a Jami’ar Yale da ke Amurka, Obasanjo ya kuma buɓaci ganin an rage tsawon wa’adin shugabannin hukumar ta INEC, da kuma ɗaukar kwararan matakai wajen naɗasu ta hanyar kaucewa baiwa waɗanda ke da ra’ayin wata jam’iya matsayi.
Dole ne Najeriya ta tabbatar da naɗin sabbin shugabannin INEC masu gaskiya a matakin ƙasa da jiha da kuma ƙananan hukumomi, tare da rage tsawon wa’adisu don dakatar da tasirin siyasa da cin hanci da rashawa, da kuma sake dawo da yarda ga tsarin zaɓe a wajen al’umma.
Obasanjo ya kuma yi nuni da yadda hukumar ta gaza yin amfani da fasahar zamani musamman na’urar BVAS da kuma ta IreV da ake amfani da ita wajen bayyana sakamakon zaɓe, a lokacin zaben shugaban ƙasar na shekarar 2023, duk kuwa da alkawuran yin hakan da shugaban hukumar ya yi
Olusegun Obasanjo Ya Nemi A Kori Shugaban Hukumar INEC Da Wasu Jami’ain Hukumar.
Tsohon shugaban na Najeriya ya ce wannan matsalar da aka samu a lokacin, ta taimaka matuka wajen tabka kura-kurai da dama a zaɓen.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
