Connect with us

News

Shugaba Tinubu Da Buhari Ne Suka Jefa Najeriya Cikin Halin Yunwa Da Rashin Tsaro Da Rashin Cigaba – Obasanjo

Published

on

Tinubu da Buhari ne suka jefa Najeriya cikin tsananin fatara da rashin tsaro – Obasanjo
tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da kuma shugaba Tinubu.

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo  ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ta gaza sakamakon shugabancin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da kuma shugaba Tinubu.

Advertisement

Obasanjo ya ce, Tinubu da Buhari ne suka jefa Najeriya cikin halin yunwa da rashin tsaro da rashin cigaba.

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

Obasanjo na waɗannan kalamai ne a yayin taron tunawa da marigayi, Chinua Achebe da ake duk shekara domin tun wa da shi wanda aka yi a jami’ar Yale da ke Amurka.

Advertisement

Tsohon shugaban ƙasar ya gabatar da wanj jawabi wanda aka naɗa, sannan aka kunna a wurin taron.

Haka kuma Obasanjo ya caccaki shugabanni biyu ta hanyar amfani da sunan da alumma suke kiran su da su na shaguɓe, wato: “Baba-go-slow” ga tsohon shugaban ƙasa Buhari da “Emilokan” ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Advertisement

“Kamar yadda za mu iya gani kuma mu fahimta, halin da ake ciki a Najeriya ya yi muni sosai. Ƙasa na daɗa lalacewa da kwatankwacin yadda ake samun ƙaruwar cin hanci da rashin tarbiyya.

Daga nan ne ake samun tashe-tashen hankula da matsalar tsaro da rarrabuwar kai da fargaba da makamantansu.

Advertisement

Waɗannan shugabanni biyu su ne suka jefa Najeriya Najeriya cikin mawuyacin halin a cewar shugaba Obasanjo.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending