Connect with us

News

Mataimakin Shugaban Kasa ”Ya Yi Amai Ya Lashe” A Kan Ambaton Sanusi II A Matsayin Sarkin Kano

Published

on

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Amai Ya LasheA Kan Ambaton Sanusi II A Matsayin Sarkin Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Cece-kuce ya barke bayan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ambaci sunan mai martaba, Muhammadu Sanusi II, a matsayin sarkin Kano na 16.

Advertisement

Daily Trust ta rawaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, ‘X’, lamarin da ya sa wasu su ka bayyana cewa ya yi biyayya tare da amincewa da sarki Sanusi a matsayin halastaccen sarkin Kano.

Pillars Da Heartland Sun Raba Maki A Filin Wasa Na Sani Abacha.

Duk da har yanzu dambarwa a kan kujerar sarkin Kano ta na gaban kotu, bangaren mai martaba Aminu Ado Bayero na cigaba da ikirarin zama halastaccen sarki duk da gwamnatin jihar Kano ta sauke shi tare da nada sarki Sanusi II.

Advertisement

New

A rubutun da ya fara wallafawa da farko, Shettima ya rubuta cewa; “a ranar Asabar, na halarci daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

“Kwankwaso ya bayar da auren ‘yar sa, Dakta Aishatu Kwankwaso ga Fahad, da wurin hamshakin dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.

Advertisement

“An daura auren ne a fadar sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II. Babban limamin masallacin fadar sarkin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen, shi ne ya jagoranci addu’ar daura auren.

“Ina taya ango da amarya murna tare da yi musu fatan samun farinciki mai dorewa a rayuwarsu ta aure.”

Advertisement

Sai dai, bayan martanin wasu mutane ma’abota amfani da manhajar ‘X’, an gyara sakon ta hanyar goge sunan sarkin Sanusi II da kuma Sarki na nawa ne ke kan mulki a yanzu.

Screenshot 20241118 142318

 

Advertisement

Sabon sakon sai ya koma; “babban limamin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen, shi ne ya jagoranci addu’ar daurin auren da aka yi a fadar sarkin Kano.”

Sai dai, duk da ya gyara sakon, wasu daga cikin ma su martani sun nuna jin dadinsu tare da jinjina masa a kan fitowa fili ya ambaci cewa Sanusi II ne sarkin Kano.

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending