Connect with us

Politics

Shugaban Jam’iyyar APC Na Karamar Hukuma GezAwa Ya Gwangwaje Daliban Da Sukayi Saukar Alqur’ani Da Kyaututtuka

Published

on

IMG 20241202 WA0016

DAGA ALIYU DANBALA GWARZO.

Alhaji Sani yamadi Shugaban jamiyyar APC na karamar Hukumar Gezawa, ya gabatar da bada tallafin a yayin Taron saukar karatun Al Quran magirma a makarantar Tarbiyyatul Aulad dake jannarya a karamar hukumar Gezawa

Advertisement

Shugaban jamiyyar yace yabada Atamfofin Tare da kudin dinki naira Dubu Dari domin kara zaburar da daliban wajen cigaba da kokarin zuwa makaranta domin samun ilimin Addini, kuma hakan zaisa sauran dalibai na baya sukara zage dantse wajen cigaba da zuwa makaranta.

Kano State Polytechnic Sun Tsunduma Yajin Aiki

yakara da cewa “hakika irin wadannan Dalibai yadace ake kokarin taimakawa duba da yadda suka maida hankali wajen zuwa makaranta har Allah yabasu damar sauke Al Qurani mai girma, dan haka babu tukuicin da yakamata ayiwa Daliban sai da irin wanan tagomashi kuma ashirye muke mucigaba da tallafawa makaratun islamiyyu da dalibai a Gezawa baki daya.

Advertisement

Kazalika yamadi yayi kira ga matasa dasu maida hankali wajen neman ilimin Addini domin shine zai taimake su a duniya da lahira.

Daga karshe yayiwa wadannan dalibai fatan Alkairi tare da Fatan zasuyi amfani da abinda suka karanta domin samarwa da kansu gobe mai kyau.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending