News
Kano State Polytechnic Sun Tsunduma Yajin Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar Malaman Kwalejin Fasaha reshen Jihar Kano, ta shiga yajin aikin gargadi na mako biyu da zai fara daga ranar 2 ga Disamba, 2024.
Wannan mataki an bayyana shi ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kungiyar, Babangida Sa’adu, ya sanya hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
Majalisar Wakilai Ta Dage Yin Muhawara Kan Dokar Haraji Har Sai Baba Ta Gani
An yanke shawarar shiga wannan yajin aikin ne a taron NEC na 112 na ASUP da aka gudanar a Abuja ranar 28 ga Nuwamba, 2024.
A lokacin wannan yajin aiki, dukkanin harkokin karatu a Polytechnic ta Jihar Kano za su tsaya cik.
ASUP ta taba bai wa gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da abin ya shafa wa’adin kwana 15 don sake duba da janye manufofin da suka saba wa dokar Polytechnics da sauran dokokin gudanarwa a wannan bangaren.
Kungiyar ta zargi Gwamnati da rashin da’a da kuma raina wasu muhimman dokokin da suka kafa manyan makarantu mallakin jihohi da sauran kayan aikin gudanarwa.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
