Connect with us

News

Zakka Kaɗai Ta Isa Ta Magance Talauci A Najeriya  —Ƙungiyar AZAWON

Published

on

images (2)

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ƙungiyar Masu Gudanar da Zakka da Waqf a Najeriya, wato AZAWON, ta bayyana cewa Zakka kaɗai ta isa ta rage yawan talauci da ya yi wa ƙasar katutu a halin yanzu.

Ƙungiyar ta yi wannan magana ne a yayin da ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi su kafa tsari mai ƙarfi na gudanar da Zakka da Waqf domin magance matsalolin tattalin arziki da talauci da ya addabi al’umma musamman a matakin ƙasa.

Zargin Rashawa : Kotu Ta Tura Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello Gidan Yari

Shugaban ƙungiyar, Injiniya Muhammad Lawal, ya bayyana hakan a taron manema labarai dangane da taron shekara-shekara na ƙasa na ƙungiyar, wanda za a gudanar daga 12 zuwa 16 ga watan Disamba a Hadejia, Jihar Jigawa.

Lawal ya ce, bisa ga rahoton Bunkasa Tattalin Arzikin Musulunci na shekarar 2015, an gano cewa damar samun kuɗaɗen Zakka na kai wa kashi 1.8 cikin ɗari na GDP na ƙasar, alhali kuwa abin da ake buƙata domin magance talauci bai wuce kashi 1.4 cikin ɗari na GDP ba.

Shugaban ya ce, kasashen da suka rungumi dabarun tattalin arzikin Musulunci na samun nasara wajen yaƙi da talauci da kuma ci gaban al’umma.

Advertisement

A cewarsa, “Dabarun tattalin arzikin Musulunci kamar Zakka da Waqf suna bayar da hanya mai ɗorewa da tasiri wajen magance waɗannan matsaloli. Zakka dai umarni ne daga Allah domin rabon dukiya da kuma magance rashin daidaito na tattalin arziki da zamantakewa.

“Zakka ba wai kawai wajibi na addini ba ne, wata hanya ce ta kawo sauyi mai kyau wanda ke haɓaka al’umma da samar da jin daɗi ga kowa.

“Saboda haka, muna kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya su kafa tsarin gudanar da Zakka da Waqf domin magance matsalolin tattalin arziki da talauci a ƙasa.

 

“Muna kuma kira ga masu hannu da shuni su bafa Zakka, wanda ya kasance ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.

Ƙungiyar AZAWON ita ce cibiyar haɗin gwiwar dukkan cibiyoyi da mutane da ke tara, raba, da sarrafa sadaka a Musulunci a Najeriya, wanda ya haɗa da cibiyoyin gwamnati, na kamfanoni, da na sarakuna a jihohi sama da 25 na tarayyar Najeriya.

Advertisement

Shugaban ya bayyana cewa taron na bana yana da taken “Amfani da Hanyoyin Musulunci Wajen Samar da Tsarin Walwala a Najeriya.

Ya ce Sakatare Janar na Dandalin Zakka da Waqf na Duniya, Dato Dr. Ghazali Mohd Nour, zai gabatar da jawabi daga hedikwatarsa a Malaysia.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending