Connect with us

News

Bana Goyon Bayan Kayyaɗe Farashin Kayayyaki – Shugaba Tinubu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce baya goyon bayan gwamnati ta karɓi ragamar kayyade farashin kayayyaki, wanda ake ganin zai sassauta farashin kayan abinci a ƙasar.

Advertisement

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke hira ta musamman da manema labarai, inda ya ce abar kasuwa ta yi halinta ta yadda hakan zai sanya farashin ya sauka.

Abubuwa Biyar Da Shugaba Tinubu Ya Yi Magana A Kai A Tattaunawa Da Manema Labarai

Bana goyon bayan ƙayade farashi, ina mai bada hakuri, abin da ya kamata mu yi shi ne mu ci gaba da samar da kayayyakin da ake buƙata a kasuwa.

Advertisement

Game da batun kudirin dokar haraji kuwa, shugaba Tinubu ya ce babu abin da zai sanya gwamnatinsa ta yi watsi da wannan doka.

Sake fasalin dokar haraji yana nan daram, alamar shugaba nagari ita ce ikon yin abin da ya kamata a lokacin da ya kamata a yi.

Advertisement

To sai dai shugaba shugaba Tinubu ya ce samakon yadda wasu gwamnoni da sanatoci ke sukar dokar, ƙofarsa a buɗe ta ke don tattaunawa a kai.

Dokar wacce a yanzu haka ta ke gaban majalisun dokokin ƙasar, ta haifar da cecekuce musamman yadda jagororin yankin Arewacin ƙasar basa goyon bayanta.

Advertisement

 

 

Advertisement

FRI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending