Connect with us

News

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Cafke Wani Ɗan Kasuwa Da Ɗaurin Hodar Iblis Masu Yawa A Kano

Published

on

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ƙasa ta (NDLEA) ta tabbatar da kama wani ɗan kasuwa wanda ya yi ƙoƙarin safarar ɗaurin hodar iblis har guda 256 a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano.

Advertisement

Daraktan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma na hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja cewa ƙwayoyin suna da nauyin kilogiram 6.

Hisbah Ta Kamo Kananun Mata 10 Da Suka Kama Dakuna A Otal

Babafemi ya ce wanda ake zargin mai suna, Chibuzo Olisaka, wanda aka kama a lokacin duba fasinjoji da ke shirin hawa jirgin Habasha ƙirar ET 941 da zai wuce ta Abidjan zuwa Kwadebuwa zuwa Addis Ababa ta ƙasar Habasa.

Advertisement

Ya ce ƙwace waɗannan kaya wanda shi ne mafi girma na hodar iblis da ta kama a Kano tun bayan kafa ofishin rundunar NDLEA ta filin jirgin Mallam Aminu Kano a shekarar 2006.

Olisaka wanda ya yi iƙirarin shi ɗan kasuwa ne mai shigo da fitar da kaya ya bi sahun waɗanda ake bincike ne a lokacin da aka samu ƙunshin ɗaruruwan hodar iblis ɗin a jikinsa.

Advertisement

Haka kuma rundunar ta yi nasarar kama wani makamancin mai wannan laifi, Akorede Olanrewaju, wanda ke ƙoƙarin fitar da ƙwayar rohypnol zuwa ƙasar Afirka ta Kudu.

Babafemi ya ce wanda ake zargin ya yi niyyar fitar da ƙwayoyin ne ta filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke jihar Legas a lokacin da jami’an rundunar suka kama mutumi.

Advertisement

An ɓoye ƙwayoyin ne a cikin wani jirgi ƙunshin kaya ɗauke da gari da takalma da singiletin mata da sauran kayayyaki.

Ko da a kwanakin baya, an samu Olarenwaju da makamancin wannan laifi a farkon wannan shekara a ranar 12 ga watan Disambar, 2023 wanda ya yi niyyar tsallakar da ƙwayar Tiramadol mai nauyin kilogiram 4.90 da kilogiram 2.10 na rohypnol zuwa ƙasar Afirka ta Kudu ta filin jirgin ƙasar Legas.

Advertisement

“Babbar kotun tarayya da ke Legas ta yanke masa shekaru biyu a gidan yari da ko zaɓin tara na Naira 900, 000, inda ya biya kuɗin kafin daga baya ya sake maimaita lafin.”

Hakazalika, jami’an rundunar NDLEA sun kama wata mata ‘yar kasuwa, Cynthia Akaeen a ranar 19 ga watan Disamba a yayin da take ƙoƙarin hawa jirgi Royal Air Maroc zuwa ƙasar Italiya ta ƙasar Habasha.

Advertisement

“An kama matar ne da ƙwayar Tiramadol har 9,190 masu nauyin kilogiram 6.00 wacce ta ce an yi mata alƙawarin Yuro 1,000 idan ta yi nasarar kai ƙwayoyin ƙasar Italiya,” in ji Babafemi.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending