Connect with us

News

Yan Sanda Sun Sanar Da Kama Shamsiyya, Da Tawagar Ta, Wadda Ake Zargi Da Ƙwarewa Wajen Satar Wayoyi A Kano.

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta sanar da kama Shamsiyya, da tawagar ta, wadda ake zaton sun kware wajen sacewa mutane wayar salula.

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi holen wata matashiya mai suna Shamsiyya da ake zargi da ƙwarewa wajen satar wayoyi a unguwanni daban-daban a Kano.

Advertisement

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Abudullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kama Shamsiyya ne ranar 21 ga watan Disamba bayan shafe tsawon shekara guda ana farautar ta.

MAƘWABCI: Rikici Kan Rabon Shinkafa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi

”Shamsiyya ta ƙware wajen ɓullo da dabarun yaudara daban-daban don hilatar mutane wajen sace musu wayoyi”, in ji sanarwar.

Advertisement

Kiyawa ya ƙara da cewa wadda ake zargin kan yi aiki ne tare da wasu mutu huɗu da ke taimaka mata ciki har da ɗan adaidaita sahu da ƙwararre wajen cire wayoyi daga makulli, wajen gudanar da ayyukanta.

”Ƙwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu kuɗaɗen daga asusun ajiyarsu na banki”, in ji SP Kiyawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending