News
Abin Fashewa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Ɗalibi Ɗaya Da Raunata Wasu A Wata Makaranta A Abuja
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wata mummunar fashewar bam ya faru a wata makaranta da ke wata unguwa a Abuja, inda ya kashe ɗalibi ɗaya kuma ya jikkata wasu huɗu, kamar yadda waɗanda suka ga abin da ya faru su baiyyana.
Wani jami’in tsaro ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a yau Litinin, a wata makarantar Islamiyya da ke unguwar Kuchibiyu, a yankin karamar hukumar Bwari, kimanin kilomita 42 daga tsakiyar birnin Abuja.
Kotu Ta Bayar Da Belin Matar Da Tayi Barazanar Kashe Dan Shugaban Kasa Tinubu, Da Shugaban Yan Sanda
Wata majiya ta ce tawagar gaggawa da jami’an tsaro, ciki har da tawogar kwararrun jami’ai masu cire bam ta ƴansanda, sun isa wurin fashewar, yayin da aka garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti.
PREMIUM TIMES ta ce rundunar ƴan sanda ba ta saki wani bayani kan lamarin ba tukuna.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
