Connect with us

News

Rundunar Ƴansanda Ta Damƙe Fasto Bisa Zargin Laifin Safarar Yara A Filato

Published

on

2ages 4 640x375

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar ƴansandan jihar Filato ta kama wata mata mai suna Nanman Pungtel da yara uku da ba ta iya bayar da cikakken bayani kan yadda ta same su a unguwar Old Airport da ke Jos ba. Wannan na zuwa ne bayan samun wasu bayanan sirri da aka miƙa wa rundunar.

Advertisement

Bayan fara bincike an kama shugaban ƙungiyar, Pastor Dayo Bernard na cocin End Time Army Ministry, wanda ya amsa laifin yin garkuwa da yara 13 daga jihar, wanda ya sayar da su akan kuɗi tsakanin ₦350,000 zuwa ₦750,000. Haka kuma, an ceto yara biyar da aka yi garkuwa da su a yankin Kwande na Qua’anpan.

Yan Ta’adda Sun Kashe Kimanin Manoma 40 A Borno

Kwamishinar harkokin mata ta Filato, Panglang Dafur, ta yi Allah wadai da rawar da wasu shugabannin addini ke takawa wajen safarar yara. Reverend Dr. Amos Mohzo na COCIN ya yi kira ga iyaye da shugabannin addini su wayar da kan al’umma kan illar wannan mummunan aikin kamar yanda Jaridar LEADSHIP ta ruwaito

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending