News
Karancin Gado A Asibitin Murtala Muhammad Na Haifar Da Barazana Ga Marasa lafiya —Bincike
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Marasa lafiya a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano na cikin mawuyacin hali, inda rashin isassun gadaje a sashen gaggawa (A&E) ke hana su samun kulawa cikin lokaci.
Malam Auwalu, wani daga cikin dangin mara lafiya, ya bayyana matsalar da suka fuskanta: “’Yata Maryam, an kawo ta asibiti ba ta cikin hayyacinta da ƙarfe 12:00 na dare.
Rundunar Ƴansanda Ta Damƙe Fasto Bisa Zargin Laifin Safarar Yara A Filato
Ba a samu gado ba ,kuma da ina da kuɗi, da na kai ta asibiti mai zaman kansa, amma dole ta sa yi mata jinya a kan benci na ƙarfe a sashen gaggawa
Aisha, wadda ta kawo kakarta Hajiya Lami, wacce ke fama da shanyewar barin jiki zuwa sashen gaggawa, ta ce, “Mun isa sashen gaggawa, amma aka ce ba a da gado.
Sai aka yi wa kakata jinya a cikin kujerar guragu na tsawon sa’o’i da dama. Abin baƙin ciki ne gani haka.”
Sai dai kuma, Aisha ta yaba wa likitoci bisa ƙoƙarinsu na yin aiki ba dare ba rana, duk da ƙalubalen rashin isassun gadaje.
Marasa lafiya da dama a sashen gaggawa sun bayyana takaicinsu, suna jin kamar ba su da wani zaɓi face jure irin wannan yanayi domin wannan asibiti ne kadai zaɓinsu.
“Sashen gaggawa na asibitin Murtala shi ne abin dogararmu don samun kulawar gaggawa. Na fi so a yi mini jinya a ƙasa da a kore ni,” in ji wani mara lafiya.
A wata hira da Kano Times, Babban Daraktan Lafiya na Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, Dr. Hussaini Muhammad, ya tabbatar da matsalar amma ya bayyana dalilan da ke haddasa cinkoson.
“Asibitin na daya daga cikin mafi rahusa kuma mafi yawan masu zuwa neman lafiya a jihar.
Mutane da dama suna tsammanin kowanne sashen gaggawa zai sami gadaje, amma ba haka lamarin yake ba.
Sashen gaggawa wuri ne na ɗan lokaci kafin a mayar da marasa lafiya zuwa sassan da suka dace, kamar sassan kashi, na magunguna, tiyata, da kuma ENT,” ya bayyana.
Dr. Hussaini ya kara da cewa: “Sashen gaggawa na iya karɓar marasa lafiya daga mutum 30 zuwa 70, wani lokacin ma mutum 50 zuwa 100. Amma muna da gadaje 36 kawai.
Yawan marasa lafiya da ke zuwa neman jinya a nan ya fi ƙarfinmu.
Dole ne mu inganta dakunan asibiti da kuma ƙara ma’aikata domin biyan buƙatun jama’a.”
Gwamnatin jihar na sane da matsalar dake tattare da sashen kiwon lafiya, kuma an yi wasu matakai don shawo kan wannan matsala. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 549.16 don shekarar 2025, inda kaso 16 (Naira biliyan 90.6) aka ware wa bangaren lafiya.
Kasafin ya kunshi gyaran gibin da ake da shi a sashen lafiya, ciki har da ɗaukar ma’aikatan lafiya da kuma gyaran cibiyoyin asibiti domin tabbatar da ingantaccen kula ga al’ummar jihar Kano.
Duk da cewa wadannan matakai suna kawo fata, ƙalubalen da marasa lafiya ke fuskanta a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ya zama faɗakarwa game da gaggawar bukatar sauye-sauye a sashen kiwon lafiya na jihar.
