Connect with us

News

Wata Budurwa Ta Rasu Sanadiyyar  Gobara Da Ta Kama Cikin Gidan Su A Kano

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wata Gobara da ta tashi a wani gida ta yi sanadiyyar rasuwar wata budurwa a unguwar Ja’en Sabere da ke karamar hukumar Gwale dake  Kano tare da konewar wasu sassan gidan.

Advertisement

Mamallakin gidan da lamarin ya faru mai suna Saminu Abba ne ya tabbatar wa manema Labarai faruwar lamarin a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairun 2025.

Kananan Hukumomi Za Su Karbi Kason Kudinsu Kai Tsaye Daga Gwamnatin Tarayya A Watan Janairu

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe daya na daren  ranar laraba , lamarin da jami’an hukumar kashe Gobara ta jihar Kano da ma yan Bijilanten yankin da sauran al’umma suka kai dauki.

Advertisement

Muna cikin Bacci muka ji wata kara da ihun mutanen unguwa, da muka tashi muka ga Gobara ce ta tashi a wasu sassan gidan mu kuma wutar ta tare hanyar da za mu fita gashi tana ci ba kakkautawa, “in ji Saminu”.

Ya ci gaba da cewa, “Bayan jami’an hukumar kashe Gobara da yan Bijilanten yankin, da sauran al’umma sun kawo musu dauki, ne aka fasa Gini ta gidan makotan su inda su shida suka fita daga gidan sai dai yar su budurwa mai shekaru 18 mai lalurar Sikila ta rasu”.

Advertisement

Mallam Saminu Abba ya kara da cewa, kayayyakin su na sawa da wasu tarin kayayyaki da dama ne suka kone kurmus, lamarin da ya nemi daukin mahukunta da su kai musu dauki bisa halin da suka samu kan su a ciki.

 

Advertisement

 

DALA FM

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending