News
Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Kano Na Neman Alhajiji Nagoda Ruwa A Jallo
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano, ƙarkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado na neman mataimaki na musamman ga gwamna kan yaɗa labarai, Alhaji Alhajiji Nagoda ruwa a jallo.
Jaridar SIYASARMU TV ta ruwaito cewa wasu matasan NNPP Kwankwasiyya ne karkashin jagorancin Zahraddin S. Kabara ne suka miƙa koke ga hukumar bisa zargin Alhajiji da wasu mutane uku da almundahanar Naira Miliyan 30 da gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya wa kungiyar Kwankwasiyya Media Forum.
Wata Daliba Ta Sa Dan Daba Ya Kai Wa Lakcara Hari A Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Kano
Cikin takardar da matasan suka miƙa, sun bukaci hukumar ta tuhumi wadanda ake ƙara domin yin bayani dalla-dalla yadda a kayi da kudaden da aka bawa ƙungiyar don tallata ayyukan gwamantin Kano.
