News
Yan Sanda Sun Cafke Ango A Ranar Ɗaurin Aurensa
DAGA MAIMUNATU BASHIR MUSA
‘Yan sanda sun kama wani mutum a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kashe wani mutum bayan sun yi faɗa a jihar Neja.
Jamilu Saidu, mazaunin unguwar Kumbashi da ke ƙaramar hukumar Mariga da ake zargi da kashe Iliyasu Aminu mai shekaru 30.
Hasken Waya Da Na Computer Na Kawo Lahani Ga Idanu —kwararren likitan ido
Jami’in rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.
Ya ce an samu wani faɗa ne da ya ɓarke tsakanin ƙauyuka biyu na Yabawa da Ungwar Sarkin-Daji, a yayin wani biki a yankin Kumbashi.
Mai magana da yawan ‘yan sandan, ya ce, Saidu ne ya sari marigayi Aminu da wuƙa a ka wanda ya jawo mutuwarsa.
“A ranar 18 ga watan Janairun 2025 da misalin ƙarfe 8:00 na yamma ne ‘yan sanda dags Bangi suka kama Jamilu Saidu da ke unguwar Kumbashi a ƙaramar hukumar Mariga saboda zargin kisan kai.”
Mista Abiodun ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma tuni aka mai da shi sashen kula da manyan laifuka (SCID) da ke Minna domin cigaba da bincike don gurfanar da shi a gaban kotu.
