News
DA DUMI DUMI : Kimanin Kananan Yara 20 Yan Ta’adda Su Kayi Garkuwa Dasu A Safiyar Wannan Rana
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Wasu mahara da ake zargin masu Garkuwa da muta ne ne sun sace Kimanin Kananan Yara 20 a garin Maradun dake jihar Zamfara.
Lamarin ya faru a safiyar Lahadi, a lokacin da yaran suka je yin itacen girki a kusa da babban asibitin Jihar .
Wani dan garin Maradun da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa da DCL Hausa cewa, maharan sun je da muggan makamai a bisa babura a lokacin da suka sace yaran.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta hannun kakakinta,Yazid Abubakar ta ce za ta bincike akan lamarin sannan ta tabbatar wa manaiba labarai.
sai dai kuma har lokacin hada wannan labarin rundunar Yan Sanda jihar bata ce komai ba akan lamarin.
Advertisements
