Connect with us

News

Mayakan M23 na kara kutsa kai yankunan gabashin Kwango

Published

on

71479648 803

DAGA IBRAHIM HOTORO 

Mayakan ‘yan tawayen kungiyar M23 na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na kutsa kai a garin Bukavu dake zama babban birnin kudancin Kivu, kwanaki bayan karbe iko da birnin Goma.

Advertisement

Mayakan na M23 dake samun goyon bayan dakarun Ruwanda a cewar rahotanni tazarar da ke tsakaninsu da garin na Bukavu bai wuce kilomita 60 ba.

Sama Da Mutane 50 Suka Mutu Sanadiyyar Harin Bam Da Aka Kai Cikin Kasuwa 

Kazalika mayakan na kuma kara nausawa ta babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke yankin, a cewar jami’in wanzar da zaman lafiya na MDD Jean-Pierre Lacroix.

Advertisement

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da fara kwashe ma’aikatanta daga wannan yanki dake da dubbunin fararen hula.

Halin da aka shiga DRC musamman ma babban birnin Goma shi ne mafi muni tun a shekarar 2012, kuma rikicin da ya samo asali sama da shekara talatin da suka gabata tun bayan yakin kare dangin Rwanda.

Advertisement

 

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending