Connect with us

News

SERAP Ta Maka Shugaba Tinubu Da Hukumar Sadarwa Ta Ƙasa NCC A Kotu Kan Yunkurin Kara Ta’azzarawa  Al’umma 

Published

on

Kungiyar SERAP Ta Bukaci Shugaba Tinubu Ya Binciki Bashin Dala Biliyan 1.5 Da Jihohi 36 Suka Karbo

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kungiyar da ke fafutukar akan yaƙi da cin hanci da rashawa da kare hakkin ɗan adam SERAP, ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya NCC, a kotu kan karan kuɗin kiran waya, saƙon tes da data zuwa kashi 50.

Advertisement

 

SERAP ta ce NCC ta amince da ƙarin, wanda ya sa kuɗin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti ɗaya, yayin da kudin sayen data 1GB ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25.

Advertisement

 

Shi kuwa kuɗin aika saƙon tes ya tashi zuwa Naira 6 daga naira huɗu da ake biya a baya.

Advertisement

 

SERAP, ta ce wannan karin an yi sa ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya saɓa wa doka tare da keta haƙƙin ’yan Nijeriya na ’yancin yin magana da samun bayanai.

Advertisement

 

A cikin ƙarar da ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, SERAP ta nemi kotu ta dakatar da aiwatar da ƙarin kuɗin, inda ta ce bai halatta ba.

Advertisement

 

ƙungiyar ta yi zargin cewa NCC ba ta bi ƙa’ida ba kuma ba ta yi la’akari da tasirin da ƙarin zai yi a rayuwar ’yan Nijeriya, waɗanda da dama ke fama da tsadar rayuwa.

Advertisement

 

SERAP, ta jaddada muhimmancin samun sadarwa cikin yanayin mai sauƙi, inda ta ce hakan wajibi ne don bai wa mutane damar amfani da haƙƙinsu na ’yancin magana da samun bayanai.

Advertisement

 

Ta ce, ƙarin zai kara tsunduma mutane cikin talauci da kuma kawo nakaso ga harkar sadarwa a faɗin Nijeriya.

Advertisement

 

ƙungiyar na roƙon kotu ta bayar da umarnin dakatar da NCCda wakilanta ko kamfanonin sadarwa daga aiwatar da ƙarin kuɗin.

Advertisement

 

Lauyan SERAP, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), ya ce wajibi ne a tabbatar da adalci, bin doka da kuma yin la’akari da yanayin da mutane ke ciki, kafin yanke duk wani hukunci da zai shafi rayuw

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending