Connect with us

News

Ba Zan Ba Ribaɗu Hakuri Ba, Inyana So Ya Kai Ni Kotun Ƙoli— Naja’atu Muhammad

Published

on

1738707497423

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce har yanzu tana nan akan bakarta kan maganar da ta fada akan mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Nuhu Ribado.

Idan za’a iya tunawa dai jaridar Inda ranka ta rawaito cewa Nuhu Ribado ya yi barazanar maka Hajiya Naja’atu Muhammad a kotu matukar bata janye kalaman da tayi a akansa ba.

Advertisement

Hajiya Naja’atu Muhammad ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da gidan Rediyon Premier dake Kano.

“Ina nan akan bakana ba zan janye kalami na ba, ballantana na ba shi hakuri, idan ya so ya kaini Kotun koli”. Inji ta

Advertisement

 

Ta ce maganar da ta fada ba karya ba ce, sai dai idan shi ne ya yiwa mutane karya lokacin da ya ke a matsayin shugaban hukumar EFCC.

Advertisement

Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce a lokacin da Nuhu Ribado yake a matsayin shugaban hukumar EFCC ya ce Tinubu cikakken dan cin hanci da rashawa ne.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending